Shugaba Karzai ya zargi NATO da rashin ba gwamnatinsa hadin kai
June 23, 2007Shugaban Afghanistan Hamid Karzai ya yi suka da kakkausan lafazi akan dakarun kungiyar tsaro ta NATO a dangane da yawan asarar fararen hula a hare haren da kungiyar ke kaiwa a Afghanistan. Karzai ya fadawa manema labarai cewa rayukan ´yan Afghanistan na da daraja kamar na sauran al´umomi. Karzai ya ce dakarun NATO ba sa neman shawarar gwamnatinsa a aikace aikacensu. Shugaban na Afghanistan ya ce idan aka ci-gaba a haka to ko shaka babu yakin da ake yi da ´yan ta´adda na cikin hadari.
O-Ton Karzai:
“Amfani da karfi fiye da kima da rashin tuntubar gwamnatin Afghanistan ke janyo asarar rayukan. Dole ne su karfafa rundunar soji da ta ´yan sandan Afghanistan tun daga toshen ta. Kamata yayi sun san cewa Afghanistan kasa ce ta dabam mai kuma al´adu dabam. Saboda haka tun daga yanzu ya zama dole su yi aiki kamar yadda mu muke bukatar su yi a nan.”
Wannan sukan ya zo ne sakamakon mutuwar fararen hula kimanin 90 sakamakon hare hare da sojojin NATO ke kaiwa a fadin kasar ta Afghanistan a cikin mako guda kacal. A kuma halin da ake ciki an halaka ´yan tawayen Taliban kimanin 60 a jerin hare hare ta sama da kuma ta kasa da dakarun kawance karkashin jagorancin NATO suka kai a lardin Paktika da ke gabashin Afghanistan.