Shugaba Karzai a Canada | Labarai | DW | 24.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Karzai a Canada

Shugaban Afganistan dake rangadin aiki a kasar Canada,yayi kira da a rufe dukkan makarantun masu zazzafan raayi na addinin islama.Dayake jawabi a birnin Montreal,Hamid karzai yace irin wadannan makarantun na koyar da kiyayyan addini ne kadai,tare da halayya na halaka wasu mutane.Bugu da kari shugaban gwamnatin na Afganistan ya kumayi kira ga kasar Pakistan data haramta ire iren wadannan makarantu,domin hurare ne na na horar da yan tarzoms.

A hannu guda kuma Sakatare general na kungiyar tsaro ta NATO,Jaap de Hoop Scheffer,yayi kira dangane da bukatar fadada ayyukan dakarun k7ungiyar a Afganistan.A hirar da wata jaridar jamus tayi dashi,jagoran kungiyar yace akwai bukatar yin hakan,domin kare Afganistan daga kasancewa sansanin horar da yan tarzoma.A jajibirin ,ranar da yan majalisar dokokin jamus zasu kada kuria dangane da makomar dakarun kasar dake Afganistan din,Mr Scheffer yayi kira ga Berlin data fadada ayyukan dakarunta a wannan kasa dake fama da barazanar yan taadda.

 • Kwanan wata 24.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5N
 • Kwanan wata 24.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5N