1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Kagame ya lashe zaɓe a ƙasarsa

August 11, 2010

Hukumar zaɓen Ruwanda, ta bayyanar da Kagame a matsayin mai nasara

https://p.dw.com/p/OisW
Shugaba Paul KagameHoto: picture-alliance/dpa

Hukumar zaɓen ƙasar Ruwanda ta ba da sanarwar cewa shugaban ƙasar mai ci, Paul Kagame ne ya samu  gagarumar nasara a zaɓen da ya gudana a ƙasar.


A wannan Larabar ne hukumar zaɓen ƙasar Ruwanda ta ba da sanarwar cewa, Shugaba Paul Kagame ne ya samu nasara a zaɓen da aka gudanar a ƙasar, wanda ake zargin an nuna danniya a cikinsa.

Sakamakon da hukumar ta bayar ya nuna cewa, Kagame wanda ke da shekaru 52 a duniya ya samu nasarar lashe kaso 93 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen da ya kasance shi ne na biyu da aka gudanar tun bayan kisan kiyashin da ya auku a ƙasar.Sai dai kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama da 'yan adawar ƙasar na zargin Shugaba Kagame da amfani da matsayinsa wajen daƙile duk wani tasiri da 'yan adawa za su yi a wannan zaɓe.

Ruanda Wahlkampf
Magoya bayan KagameHoto: DW

Salim Ahmed Salim, shi ne jagoran tawagar masu sanya idanu a zaɓen daga ƙungiyar ƙasashe renon ingilishi wato Commonwealth.Ya ce ko da yake an gudanar da  zaɓen cikin tsari, za a iya cewa akwai ƙarancin 'yan adawa a cikinsa, domin dukkanin 'yan takara huɗu da suka shiga zaɓen, sun fito ne daga jam'iyyun haɗaka na gwamnati.

Yawancin jam'iyyun adawar da ke yin zargin an nuna musu danniya, sun ce an yi ƙoƙarin toshe duk wata hanya da suka bi na ganin sun sami rejistar shiga wannan zaɓe.Gabanin zaɓen ne aka halaka mataimakin shugaban ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun adawar ƙasar da kuma wani ɗan jarida da ke yin kakkausar suka ga gwamnatin Kagame. Hakazalika an rufe gidajen jaridu biyu na 'yan adawa, tare da kama 'yan adawar da 'yan jaridu da dama bisa tuhume-tuhume daban-daban.

Amma kuma duk da waɗannan al'amura, shugaba Kagame ya ce an gudanar da zaɓen bisa gaskiya da adalci. Haka su ma masu goyan bayan Shugaba Paul Kagame, sun danganta wannan nasara tasa ga irin ci-gaban da ƙasar ta samu ta fannin tattalin arziƙi da zaman lafiya a ƙarƙashin mulkinsa.

FLASH-GALERIE Ruanda Wahl 2010 Paul Kagame
Shugaba Paul Shugaba a tsakiya, yayin bukin samun nasararsa.Hoto: AP

Shugaba Paul Kagame ya fara mulkin ƙasar Ruwanda ne, tun bayan lokacin da ƙungiyarsa ta 'yan tawayen ƙabilar Tutsi da aka fi sani da Rwandan Patriotic Front, ta tarwatsa 'yan tawayen ƙabilar Hutu da suka halaka 'yan kabilar Tutsi kusan 800,000 a kisan kiyashin da ya auku a shekarar 1994.

Mawallafiya: Halima Sani Umar

Edita: Halima Balaraba Abbas