Shugaba Kabila da mataimakinsa sun yi kira da a kwantar da hankali | Labarai | DW | 28.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Kabila da mataimakinsa sun yi kira da a kwantar da hankali

Kwana daya gabanin zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a JDK, ´yan takara biyu a zaben sun yi kira ga magoya bayansu da su kwantar a hankulansu. A cikin wata sanarwar hadin guiwa da suka bayar shugaba Josef Kabila da mataimakinsa Jean-Pierre Bemba sun yi alkawarin yin bakin kokarinsu wajen tabbatar da cewa zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana, kana kuma zasu amince da sakamakonsa tare da shawo kan jama´a da su wanzar da zaman lafiya da juriyewa juna. Tun bayan bayyana sakamakon zagaye na farko na zaben shugaban kasa a ciin watan agusta, Kongo wadda take kasa ta 3 mafi girma a nahiyar Afirka ke fama da tashe tashen hankula musamman tsakanin magoya bayan ´yan takarar su biyu. Akalla mutane 20 aka kashe a fadace fadace tsakanin sassan biyu a birnin Kinshasa.