Shugaba Köhler ya fara ziyarar kwanaki 10 a Africa | Labarai | DW | 04.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Köhler ya fara ziyarar kwanaki 10 a Africa

A wani lokaci ne a yau din nan shugaban kasar Jamus, Hörst Köhler aka shirya cewa zai sadu da tsohon shugaban kasar Africa ta kudu, wato Mr Nelson Mandela a can kasar Mozambique.

Hakan dai yazo ne aci gaba da ziyarar shugaban kasar ta Jamus na tsawon kwanaki uku a kasar ta Mozambique.

Babbar dai ajandar kai wannan ziyara shine a kulla dangantakar siyasa da kuma ciniki a tsakanin kasar ta Jamus da kuma Mozambique.

A wani jawabi daya gabatar, shugaban na Jamusawa ya tabbatar da cewa Mozambique kasa ce da kasashen Africa yakamata suyi koyi da ita, wajen yadda take yaki da matsaloli na siyasa da kuma talauci ba tare da taimakon wata kasa daga ketare ba.

Shugaba Köhler, wanda ke gudanar da ziyarar da tawagar Jamusawa yan kasuwa, an shirya cewa zai kai irin wannan ziyara izuwa kasashen Madagascar da kuma Botswana.