1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Jacob Zuma zai fuskanci hukunci

October 13, 2017

Kotun kolin Afirka ta Kudu ta ce shugaba Zuma na iya fuskantar hukunci kan tuhume-tuhume masu nasaba almundanar dala biliyan 5 na Amirka, na cinikin makamai da ya yi tun cikin shekarun 1990.

https://p.dw.com/p/2lnPQ
Südafrika Präsident Jacob Zuma
Hoto: Getty Images/AFP/R. Jantilal

Kotun kolin kasar Afirka ta Kudu ta ce shugaba Jacob Zuma na iya fuskantar hukunci kan tuhume-tuhume akalla 800 masu nasaba almundanar dala biliyan 5 na Amirka, na cinikin makamai da ya yi tun cikin shekarun 1990. Yanzu dai ma'aikatar shari'ar kasar na da jan aiki gabanta na daukar matakin doka da bisa ga alamu shugaba zuma ke hangen jarum.

Shi dai shugaban na Afirka ta Kudu ya sha musanta zarge-zargen da ake masa, wadanda ya ce an yi su ne tun lokacin da yake tasowa cikin jam'iyyar ANC. Jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance ce dai ta sha kai gwauro da mari tun kimanin shekaru takwas da suka gabata, na ganin Mr. Zuma ya fuskancin shari'a. Akwai ma wasu manyan jami'an gwamnati da ke cikin wannan badakala, bayan shi shugaba Zuma.