1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Jacob Zuma na cikin tsaka mai wuya

Salissou Boukari
February 13, 2018

Jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afrika ta Kudu ta bai wa Shugaba Jacob Zuma kwanaki biyu na ya yi murabus, bayan da aka gaza samun matsaya a tattauwar da aka kwashe tsawon lokaci.

https://p.dw.com/p/2sZpo
Südafrika Jacob Zuma
Shugaba Jakob Zuma na Afrika ta KuduHoto: picture-alliance/dpa/EPA/A. Ufumeli

Wasu kafofin yada labaran kasar sun ce jam'iyyar ta ANC za ta aike wa Shugaba Jacob Zuma wasikar cewa ya sauka daga karagar mulkin kasar bayan da ta yi watsi da bukatar shugaban na cewa a barshi a kan mukaminsa har na tsawon 'yan watanni.

Sai dai har wannan lokaci jam'iyar ta ANC ba ta sanar da wannan labari a hakumance ba, amma kuma ta kira wani taron manema labarai da misalin karfe 12 agogon kasar karfe 10 agogon GMT a cibiyarta da ke birnin Johannesburg. A shekara ta 2008 ma dai jam'iyyar ta ANC ta saukar da Shugaba Thabo Mbeki wanda ya yi biyayya ga hukuncin jam'iyyar ta hanyar yin murabus. Sai dai kuma ba wai tilas ne ba ga shugaban kasa ya amince da hakan ba.