Shugaba Iarn ya ce kasarsa zata ci-gaba da samar da makamashin nukiliya | Labarai | DW | 03.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Iarn ya ce kasarsa zata ci-gaba da samar da makamashin nukiliya

Rundunar sojin Amirka ta ce wani bincike da ta gudanar akan zargin yiwa fararen hula kisan gilla cikin watan maris a garin Ishaqi dake Iraqi, ya wanke sojojin ta daga wannan zargi. Da farko jami´an Iraqi sun ce sojoji Amirka sun harbe mutane 11 dukkan ´yan gida guda a wani samame da suka kai cikin wani gida, wanda daga bisani aka kai masa harin makami mai linzami. Binciken da Amirka ta yi ya gano cewar mutum 4 kadai aka kashe. Mataimakin hafsan dakarun kasa da kasa a Iraqi, manjo Janar William Caldwell ya fadawa wani taron manema labarai a birnin Bagadaza cewa sojojin Amirka ba su aikata wani laifi ba, a saboda haka ba za´a sake gudanar da sabon bincike ba.