Shugaba Hu yana Liberia | Labarai | DW | 01.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Hu yana Liberia

Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya isa kasar Liberia,wanda ke zama kasa ta biyu daya sa kafa ,a rangadin aikin daya fara a kasashe guda 8 na nahiyar Afrika ,domin inganta danganta tsakanin Sin din na Nahiyar.Shugaban na Sin zai tattauna da shugaba Ellen Johnson Sirleaf .Kazalika anasaran shugabannin biyu zasu rattaba hannu a yarjeniyoyi da zasu hadar da kasuwanci da ilimi da harkokin lafiya.Daga Liberioan dai anasaran Shugaba Hu zai wuce kasar Sudan mai arzikin man petur,inda akesaran ganin irin rawa da zai taka wajen kokarin da akeyi na shawo kann gwamnatin Khartum adangane da tura dakarun kiyaye zaman lafiya zuwa lardin Darfur.