Shugaba Hu Jintao na ƙasar Sin ya kammala ziyarar kwana 4 a Indiya. | Labarai | DW | 23.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Hu Jintao na ƙasar Sin ya kammala ziyarar kwana 4 a Indiya.

A yau ne shugaba Hu Jintao na ƙasar Sin, yake kammala ziyarar kwana 4 da yake kai wa ƙasar Indiya. Da yake yi wa shugabannin masana’antu jawabi a birnin Mumbai, Hu Jintao ya ce kamata ya yi ƙasashen biyu su yi duk iyakacin ƙoƙarinsu wajen inganta hulɗoɗin cinikayya tsakaninsu. Ya ƙara da cewa, a wannan ƙarnin, nahiyar Asiya, za ta iya jagorancin sauran ƙasashen duniya. Amma kafin hakan ya tabbata, sai Sin da Indiya sun kau da shinge a harkokin cinikayya tsakaninsu.

Ƙasashen biyu, waɗanda suka fi ko wace ƙasa yawan al’umma a duniya, sun sha samun hauhawar tsamari tsakaninsu tun 1962, yayin da suka gwabza wani yaƙi a kan iyakarsu. ’Yan gudun hijiran yankin Tibet da dama ne suka yi ta zanga-zanga a lokacin ziyara shugaba Hu a Indiyan. A wajen masaukin shugaban a birnin Mumbai ma, rahotanni sun ce wani ɗan gudun hijiran Tibet ɗin, ya cinna wa kansa wuta, don nuna adawa ga ci gaba da mamaye yannkin da Sin ke yi har ila yau. Sai dai ’yan sanda sun iya kashe wutar kafin ta cinye shi, inji rahotannin.

Shugaba Hu, zai ci gaba da ziyararsa ne a ƙasar Pakistan.