1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Hu Jintao na ƙasar Sin, ya isa a Pakistan bayan ziyarar da ya kai a Indiya.

November 23, 2006
https://p.dw.com/p/Buae

Shugaba Hu Jintao na ƙasar Sin, ya sauka a birnin Islamabad a ci gaba da ziyararsa a wasu kasashen Asiya. Shugaban dai ya fara ya da zango ne a ƙasar Indiya, inda ya shafe kwanaki 4, yana shawarwari da mahukuntan birnin New Delhi a kan jigon inganta hulɗodin cinikaya tsakaninsu. A Pakistan ɗin ma, babban jigon tattaunawar da zai yi da shugabannin ƙasar, zai duƙufa ne kann bunƙasa harkokin tattalin arziki tsakanin Beijing da Islamabad. Ana dai kyautata zaton cewa, shugaba Hu da takwaran aikinsa na Pakistan Pervez Musharraf, za su sanya hannu kan wata yarjejeniya ne ta kafa wani shacin kasuwanci maras shinge tsakanin ƙasashensu biyu, yarjejeniyar da in ta fara aiki, za ta riɓanya harkokin cinikayyar Sin da Pakistan har sau uku a cikin shekaru 5 masu zuwa nan gaba. Ziyara da shugaba Hu dai, ita ce ta farko da wan9i shugaban Sin ya taɓa kai wa Pakistan ɗin tun shekaru 10 da suka wuce.