Shugaba Htin Kyaw na Myanmar ya kama aiki | Siyasa | DW | 30.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shugaba Htin Kyaw na Myanmar ya kama aiki

An rantsar da Htin Kyaw a matsayin sabon shugaban kasar Myanmar na farar hula bayan kasar ta kwashe kimanin shekaru 50 karkashin mulkin sojoji.

Myanmar Vereidigung der neuen Regierung in Naypyidaw

Rantsuwar kama aiki a Myanmar Shugaba Htin Kyaw a tsakiya

Sabon shugaban Htin Kyaw tare da mataimakansa biyu da Myint Swe da Henry Van Thio gami da ministoci 18 sun yi rantsuwar kama aiki a zauren majalisar dokokin kasar.

Shugabar jam'iyyar NLD mai mulki Aung San Suu Kyi ta kasance sabuwar ministar harkokin waje wadda take da ma'aikatu uku karkashin ikonta. Shugaba Htin Kyaw ya karbi madafun ikon kasar ta Myanmar ko Bama daga hannun tsohon Shugaba Thein Sein, wanda ya aiwatar da sauye-sauye da suka kai kasar bisa tafarkin demokradiyya. Jam'iyya mai mulki ta NLD ta samu gagarumar nasara yayin zaben da ya gabata, kuma mambobin majalisar dokokin ne suka zabi sabon shugaban kasar a cikin wannan wata na Maris.

Myanmar Htin Kyaw Staatspräsident mit Aung San Suu Kyi Parteivorsitzende

Shugaba Htin Kyaw da Aung San Suu Kyi

Yayin jawabi a cikin majalisar dokoki, sabon shugaban Htin Kyaw ya yi alkawarin hada kan 'yan kasa:

"Sabuwar gwamnatin za ta aiwatar da sauye-sauye demokaradiyya karkashin tsrarin mulki, tsarin mulkinmu zai tabbatar da sasantawa gami da zaman lafiya, da samar da tsarin tarayya, tare da rayuwa mai inganci ga mutane."

Sannan sabon shugaban ya nuna muhimmancin gyara ga kundin tsarin mulkin domin ya dace da rayuwar 'yan kasar:

"Ina da aiki na gyara ga tsarin mulki, saboda ya zama irin na rayauwar kasarmu tare tsarin demokaradiyya."

Rantsar da sabon shugaban Htin Kyaw na zama wani abu na tarihi ga kasar ta Myanmar mai mutane kimanin milyan 54, kuma daya daga cikin 'yan rabbana ka wadatamu da ke yankin Kudu maso Gabashin Asiya. Thiri Yadana ta kasance 'yar majalisar dokoki ta kasar wadda ta nuna jin dadi da kalaman sabon shugaban kasar:

Myanmar Parlament wählt neuen Präsidenten

'Yan majalisar dokokin Myanmar

"Lokacin da na saurari jawabin sabon shugaban kasa na farar hula, jawabin na da kyau, duk majalisa da kasa mun ji jawabin da ba a taba ji ba, mun ji abin da babu wanda ya taba ji."

Ita dai shugabar jam'yyar NLD mai mulki Aung San Suu Kyi 'yar shekaru 70 da haihuwa, kuma sabuwar ministar harkokin waje, kundin tsarin mulkin kasar ta Myanmar ya haramta mata zama shugabar kasa, saboda tana da 'ya'ya wadanda suke 'yan wata kasa, amma ta ce ita ce mai madafun iko kuma ana sa ran sabon shugaban Htin Kyaw ya aiwatar da manufofin da take goyon baya.

Sauti da bidiyo akan labarin