1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Hollande na halartar taron tsaro a Najeriya

Yusuf BalaMay 14, 2016

Shugaba Muhammadu Buhari mai masaukin baki zai gana da Shugaba Hollande a birnin na Abuja fadar gwamnatin Najeriyar.

https://p.dw.com/p/1Inmy
Nigeria Francois Hollande trifft den nigerianischen Außenminister Geoffrey Onyeama
Shugaba Hollande a tsakiya bayan da ya isa NajeriyaHoto: Reuters/A. Sotunde

A ranar Asabar din nan ce Najeriya ke bude taron tattaunawa da kasashe makobtanta da kasashen Yamma a kokari na aikin hadin gwiwa na ganin an kawo karshen aiyyukan ta'addanci da ke tagayyara kasar da makobtanta.

Shugabannin da za su hadu a wajen taron sun hadar da shugaban jamhuriyar Benin da Kamaru da Cadi da Nijar, yayin daga kasashen Yamma shugaba Francois Hollande da mataimakin sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken da ministan harkokin wajen Birtaniya Philip Hammond ke halarta.

Shugaba Muhammadu Buhari mai masaukin baki zai gana da Shugaba Hollande a birnin na Abuja fadar gwamnatin Najeriyar. Dukkanin kasashen biyu dai sun rattaba hannu kan yarjejeniyar aiki tare inda za su rika musayar bayanai na soji a kokarin da Faransa ke yi na ganin an samu mafita a rikici da mayakan na Boko Haram.

Wannan taro dai na zuwa ne bayan wanda aka yi kan wannan matsala ta tsaro a Paris shekaru biyu kenan.