1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

SHUGABA GADDAFI A BRUSSELS.

A yau ne shugaban kasar Libya, Muammar Gaddafi, ya fara wata ziyarar aiki a nahiyar Turai. A birnin Brussels ne dai ya ya da zango, inda shugaban Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turai, Romano Prodi, ya tarbe shi da hannu biyu-biyu. Shugaban na Libya, zai yi shawarwari ne da kusoshin kungiyar, inda kuma zai nemi shigar kasarsa cikin rukunin ma’ammalar tattalin arzikin nan na kasashen yankin bahar Rum da Kungiyar ta Hadin Kan Turai. Wannan ziyarar dai, ita ce ta farko da shugaba Gaddafi, ya taba kawowa a nahiyar Turai, tun shekaru 15 da suka wuce.

Shugaba Gaddafi, da Romano Prodi, shugaban Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turai, yayin da yake yi masa marhaba a birnin Brussels.

Shugaba Gaddafi, da Romano Prodi, shugaban Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turai, yayin da yake yi masa marhaba a birnin Brussels.

A lokacin da farar marsandin da ta dauko shugaba Gaddafi daga filin jirgin saman birnin Brussels, ta isa a hedkwatar kungiyar Hadin Kan Turai, magoya bayansa da dama sun taru gaban ginin, rike da koriyar tuta ta kasar Libyan, suna kuma kade-kade da wake-waken gargajiya, don yi masa marhaba. Ya dai juya ya cira musu hannu, kafin ya shiga shawarwari da shugaban Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turan, Romano Prodi. Amma, yayin da shugaba Gaddafi ke cikin ginin, sai da masu kare lafiyarsa suka yi gwagwarmaya da wani daga cikin magoya bayansa, wanda ya kutsa har zuwa kusa da shi, yana son ya mika masa wata takarda.

Wannan dan rudamin da aka samu dai, bai hana shugaba Gaddafin da Romano Prodi ci gaba da huldarsu ba. Sun yi murmushi abinsu, gaban masu daukan hotunan talabijin da sauran `yan jarida, kamar ma babu abin da ya auku. A can waje kuma, nesa kadan daga ginin Hedkwatar kungiyar Hadin Kan Turan, wasu `yan gudun hijiran Libyan, masu adawa da shugaba Gaddafi, sun yi zanga-zangar nuna bacin ransu ga ci gaba da keta hakkin dan Adam da suka ce har ila yau ana yi a kasarsu, abin da kuma kungiyar fafutukar kare hakkin dan Adam nan Amnesty International ta jaddada, kafin ma shugaba Gaddafin, ya iso a birnin Brussels.

Masu zanga-zangar dai sun yi ta kururuwa a kan titi inda suke cewa, Gaddafi dan mulkin kama karya, kuma azzalumi.

Tun 1969 ne dai shugaba Gaddafi, wanda a lokacin yake da shekaru 28 da haihuwa, ya hau karagar mulkin kasar Libyan, bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yi. Tun hawarsa mulkin dai, shugaba Gaddafi, ya zame wa kasashen Turai da Amirka, kamar wata sarkakkiya a jika. Sun dai sha sukarsa da daure wa `yan ta’adda gindi. Amma a wannan ziyarar da ya kawo a birnin Brussels, shugaba Gaddafi ya bayyana dalla-dalla cewa, ba shi da wata jibinta da `yan ta’adda. Duk wadanda suka sami horo a kasarsa, `yan fafutukar neman kwatar `yancin kasashensu ne. Ya kara da cewa:-

"Mun dau nauyin da ya rataya a wuyarmu. Mun bai wa mayakan neman kwatar `yancin horon soji, don su iya samar wa kansu `yanci. Mun dai yi imanin cewa, wannan wani nauyi ne da ya rataya a wuyarmu, a tarihi."

Kafin dai a sami sassaucin tsamari tsakanin kasashen Yamma da Libyan, sai da Shugaba Gaddafi, ya biya dimbin yawan kudaden diyya na kimanin dola biliyan 2 da digo 8, ga Amirka da Faransa, saboda dasa bam din da aka yi a cikin jiragen samansu, wadanda kuma aka zargi Libyan da samun hannu a ciki. A cikin shekarar 1986 kuma, an zargi `yan ta’addan Libyan da ta da bam a wani gidan rawa a birnin Berlin. Har ila yau dai, ana ci gaba da tattaunawa kan diyyar da Libiyan za ta biya game da wannan batun. Ministan harkokin wajen Jamus, Joschka Fischer, ya ce ba zai mika wa shugaba Gaddafi hannu ba, sai an cim ma madafa kan wannan batun. Ya dai kyautata zaton cewa, nan ba da dadewa ba za a cim ma daidaito. Joschka Fischer ya kara bayyana cewa:-

"Muna fata dai, za a cim ma yarjejeniya, don nuna mutunci ga duk wadanda abin ya shafa, don kuma nuna adalci ga `yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a wannan harin. Libyan da kanta ma na da sha’awar ganin cewa, an cim ma daidaito, saboda yunkurin da take yi na sake samun karbuwa a gamayyyar kasa da kasa."

Ministan ciniki na kasar Libiyan, Abdelkader Omar Blikhair, ya yi kira ga kungiyar Hadin Kan Turai, da ta bi misalin Amirka, wajen dage takunkumin tattalin arzikin da ta sanya wa kasarsa. Amirka dai ta ce za ta soke sunan Libiya, daga jerin kasashen da ta ce suna tallafa wa yaduwar ta’addanci a duniya. A cikin watan Disamban bara ne Libiyan ta sake alkibla, ta ba da sanarwar cewa, za ta janye daga duk wani yunkurin mallakar makaman kare dangi. Ta kuma mika duk wasu na’urorin sarrafa makaman nukiliyan da take da su ga Amirka. A cikin jawabin da ya yi wa maneman labarai dai, shugaba Gaddafi ya bayyana cewa:-

"A halin yanzu dai, Libiya, wadda ta jagoranci mayakan neman kwatar `yanci a nahiyar Afirka da kuma kasashe masu tasowa, ta yanke shawarar jagorancin fafutukar samad da zaman lafiya a duniya."

Da wannan ziyarar da shugaba Gaddafi ya kawo a Turai, a karo na farko tun shekaru 15 da suka wuce dai, za a iya cewa, kasarsa ta sami karbuwa a gamayyar kasa da kasa. Shugaban Hukumar kungiyarr Hadin Kan Turai,Romano Prodi, ya yi wa shugaba Gaddafi kyakyawan yabo a cikin jawabinsa na marhaba. Ya kuma shawarci kungiyar da ta karbi Libiya cikin rukunin kasashen nan na yankin bahar Rum, ba da wani bata lokaci ba kuma.

 • Kwanan wata 27.04.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvkD
 • Kwanan wata 27.04.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvkD