Shugaba Fidel Castro na Cuba ya mika ragamar mulki | Labarai | DW | 01.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Fidel Castro na Cuba ya mika ragamar mulki

Shugaban ƙasar Cuba Fidel Castro ya mika ragamar mulkin kasar na wucin gadi ga dan uwan sa Raul Castro kuma ministan tsaro na ƙasar Cuba. Fidel Castro wanda ke fama da jinya ya gabatar da jawabi ga alúmar ƙasar wanda aka karanta a madadin sa. A cikin jawabin Castro ya yi kira ga jamaár ƙasar su jajirce a kan ƙasar Amurka su kuma kasance tsintsiya madaurin ki ɗaya. Yace ya yi Imani alúmar ƙasar a bisa aƙidar da suka sanya a gaba, ba zasu bari Amuka ta yi musu shiga hanci da ƙudundune ba. Castro wanda a ranar 13 ga wannan watan zai cika shekaru 80 a duniya ya buƙaci ɗage bukukuwan zagayowar ranar haihuwar sa ya zuwa 2 ga watan Disamba wanda ya yi daidai da shekaru 50 tun bayan da ya ƙaddamar da yaƙin sunkuru a gabashin Cuba.