Shugaba Ellen ta Liberia ta fara ziyara a Ivory Coast | Labarai | DW | 29.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Ellen ta Liberia ta fara ziyara a Ivory Coast

Zababbiyar shugabar kasar Liberia, wato Ellen Jonhson Sirleaf ta isa kasar Ivory Coast a yau talata don kara inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Wannan dai ziyara ta kasance irin ta ta farko a tun lookacin data lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar zagaye na biyu, wanda hakan ya bata damar kasancewa mace ta farko da zata rike madafun iko a matsayi na shugaban kasa.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa Ellen Johnson ta samu tarba ne ta musanman daga shugaban kasar ta Ivory Coast wato Lauret Gbagbo tare da jami´an gwamnatin sa a filin jirgin saman Abidjan.