Shugaba Chirac ya sake nuna goyon baya ga bin hanyoyin lumana akan rikicin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 23.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Chirac ya sake nuna goyon baya ga bin hanyoyin lumana akan rikicin nukiliyar Iran

Shugaban Faransa Jacques Chirac ya ce yana kyautata zaton cewar za´a gano bakin zaren warware fito na fiton da ake yiwa da Iran game da shirin nukiliyarta ta hanyar yin shawarwari. Shugaba Chirac ya fadawa wani taron manema labarai na hadin guiwa da suka yi da shugabannin Jamus da Rasha cewa galibi ra´ayi ya zo daya cewar bin hanyoyin lumana wajen shawarari ne kadai zai kai ga warware wannan kiki-kaka cikin ruwan sanyi. Shugabannin Faransa da Jamus da Rasha na wani taro ne yau a arewacin Faransa don duba damuwar da kasashen yamma ke nunawa game da rikicin makamashi da kuma sabbin manufofin tattalin arziki da gwamnatin Mosko ke aiki da su.