Shugaba Chavez ya sake lashe zaben kasar Venezuela | Labarai | DW | 04.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Chavez ya sake lashe zaben kasar Venezuela

Ruwan sha mai tsabta

Ruwan sha mai tsabta

Shugaban Venezuela Hugo Chavez ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar jiya don yin wani sabon wa´adin shugabanci na shekaru 6. Bayan kammala kidayar sama da kashi 70 cikin 100 na yawan kuri´un da aka kada, Chavez ya samu kashi 61 yayin da babban abokin adawa Manuel Rosales ya samu kashi 38 cikin 100, inji hukumar zaben kasar. Tuni kuwa har mista Rosales ya amince da shan kaye a zaben. A jimilce ´yan kasar ta Venezuela su miliyan 16 ne suka kada kuri´a a zaben na jiya lahadi. Shi kuwa a nasa bangaren shugaba Chavez ya fara bukin nasarar da ya samu, inda ya fadawa magoya bayansa cewa zai ci-gaba da bin wani sabon salo na tsarin gurguzu. Masu sa ido a zabe na kasa da kasa sun yaba da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana.