Shugaba Chavez na Venezuela ya yi jawabi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya. | Labarai | DW | 21.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Chavez na Venezuela ya yi jawabi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Shugaban ƙasar Venezuela, Hugo Chavez, ya yi jawabi ga taron ƙoli na Majalisar Ɗinkin Duniya abirnin New York, inda ya yi amfani da damar wajen yin kakkausar suka ga Amirka. Shugaban ya ce Amirka dai ta zamo wa Majalisar wani alaƙaƙai ne, saboda tana hana ta gudanad da aikinta kamar yadda ya kamata, kuma tana ƙara cin zarafin ƙananan ƙasashe matalauta.

Shugaba Chavez ya kuma la’anci takwaran aikinsa na Amirka, Gerge W. Bush, inda ya kira shi riƙaƙƙen shaiɗani, mai ɗoyin farar wuta. A gabnin Chavez dai, Bush ne ɗan mulkin kama karya na farko a duniya, wanda kuma yake bukatan likitan mahukata ya yi masa jiyya. Wasu daga cikin wakilan da ke halartar taron, sun yi ta wa shugaba Chavez taɓi a lokacin da yake jawabinsa. Amma sakatariyar harkokin wajen Amirka, Condoleeza Rice, ta ce babu abiin da ya gamsad da ita da jawabin na shugaba Chavez. Ta ce ba za ta ma ɓata lokacinta wajen mai masa da martani ba.