1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Bush yayi kira da a shirya taron kwamitin Sulhu dangane da rahoton Mehlis

October 22, 2005
https://p.dw.com/p/BvOQ

Shugaban Amirka GWB ya yi kira ga kwamitin sulhu na MDD da ya hanzarta daukar matakai akan Syria bayan wani binciken da majalisar ta yi ya nuna cewa da akwai hannun hukumomin leken asirin Syria da Lebanon a kisan gillar da aka yiwa tsohon FM Lebanon Rafik Hariri. Bush na tofa albarkacin bakin sa ne akan rahoton binciken da babban alkalin Jamus Detlev Mehlis yayi dangane da kisan gillar da aka yi wa Hariri da kuma wasu mutane 20 a ranar 14 ga watan fabrairu. Rahoton ya nunar da cewa an aikata wannan danya ce tare da sanin mayan jami´an hukumar leken asirin Syria da kuma Lebanon. Tuni dai gwamnatin Syria a birnin Damaskus ta yi watsi da zargin tana mai cewa yana da wata manufa ta siyasa. Shi ma shugaban Lebanon mai samun goyon bayan Syria Emile Lahud ya musanta cewa yana da hannu a wannan kisa.