1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Bush ya yi taron manema labarai a fadar White House

June 14, 2006
https://p.dw.com/p/Butx

Shugaban Amirka GWB ya yi kashedin cewa duk da ci-gaban da ake samu a Iraqi, zai zama rashin tunani a yi fatan kawo karshen tashe tashen hankula nan take. Bush na magana ne a wani taron manema labari a fadar White House kawan daya bayan ziyarar ba zata da ya kai birnin Bagadaza, inda ya gana da FM Nuri Al-Maliki. Bush ya ce Amirka zata cika alkawarinta na taimakawa Iraqi, to amma ya kara da cewa hakan zai dogara ne akan karfin gwamnatin Iraqi da kuma yadda dakarun tsaronta za su kara daukar nauyin dake kansu. A gun taron manema labaran shugaba Bush ya yi tsokaci game da sabbin matakan da ake dauka da nufin maido da tsaro a cikin kasar.

“Ya ce: da sanyin safiyar yau aka fara wannan gagarumin aiki na hadin guiwa da zumar maido da tsaro da bin doka a wurare da dama na babban birnin kasar. Mun girke sojojin Iraqi kimanin dubu 26 da ´yan sanda dubu 23 hade da dakarun kawance a birnin na Bagadaza, mai mazauna sama da mutum miliyan 6.5. Dole ne mu kwana da sanin cewa za´a dauki lokaci mai tsawo ana gudanar da wannan aiki.”