1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Bush ya yi kira ga Sineta Kerry daya nemi gafara´r sojin Amirka

November 1, 2006
https://p.dw.com/p/Budi
Kwanaki kalilan gabanin zaben ´yan majalisun dokoki da za´a yi a Amirka, shugaba GWB ya zargi tsohon dan takarar shugaban kasa na jam´iyar democrat John Kerry da cin mutuncin sojin Amirka. Bush ya bayyana kalaman da Kerry ya yi da cewa wani abin kunya ne da cin fuska. A jawabin da yayi jiyaa a gaban dalibai a birnin Los Angeles sineta Kerry yayi kira garesu da su nuna kwazo da himma musamman wajen neman ilimi idan ba haka ba to zasu kare ne a kasar Iraqi. A martanin da ya mayar shugaba Bush cewa yayi.
“Kalaman da sinetan yayi cewa sojojinmu ba su da cikakken ilmi cin mutunci ne kuma abin kunya ne. Sojoji rundunar Amirka mutane ne masu hazaka da kwazo saboda haka ya zama dole sinatan daga Massachusettes ya nemi gafarsu.”