Shugaba Bush ya yi garambawul a wasu muƙamai cikin gwamnati | Labarai | DW | 05.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bush ya yi garambawul a wasu muƙamai cikin gwamnati

Shugaban Amirka GWB ya ba da sanarwar yin wasu canje canje na muhimman mukamai guda biyu. John Negroponte wanda kawo yanzu ya ke rike da mukamin daraktan hukumar leken asiri ta kasa yanzu an nada shi a mukamin mukaddashin sakatariyar harkokin waje. Yayin da aka maye gurbinsa a mukamin daraktan hukumar leken asirin da Vice Admiral Michael McConnel mai ritaya. Dole sai majalisar dattijai ta amince da dukkan mukaman guda biyu.

A kuma kwanaki kalilan masu zuwa ake sa ran Bush zai bayyana sabbin manufofinsa dangane da Iraqi. Kafofin yada labarun Amirka na yada jita-jitar cewa shugaban zai ba da sanarwar karin yawan sojoji kimanin dubu 20 na wucin gadi a Iraqi.