1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Bush ya sha kaye a majalisar dattawa

December 17, 2005
https://p.dw.com/p/BvGB

A wani labarin kuma majalisar dattijan Amirka sun kada kuri´ar kin amincewa da wani shirin shugaba Bush na sabunta dokar tabbatar da kishin kasa wato Patriotic Act. A daura da haka ´yan adawa na jam´iyar democrat da takwarorinsu na republicans sun kara matsa kaimi a bukatunsu na inganta dokokin tsaron lafiyar jama´a. Jim kadan bayan hare haren 11 ga watan satumban shekara ta 2001 aka kafa dokar ta tabbatar da kishin kasa, wadda ake gani ta zama kashin bayan yaki da ta´addaci da shugaba Bush ya kaddamar.