Shugaba Bush ya gana da Angela Merkel a garin Stralsund. | Labarai | DW | 13.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bush ya gana da Angela Merkel a garin Stralsund.

A ziyarar da yake kawo wa Jamus, shugaban Amirka George W. Bush, ya gana da shugaban gwamnatin tarayya Angela Merkel a garin Stralsund. A taron maneman labarai da suka kira bayan ganawar, shhugabannin biyu sun ce sun tattauna batun ce-ce ku cen da ake yi ne da Iran, kan shirinta na mallakar makamashin nukiliya, da rikicin da ake yi da Korea Ta Arewa da kuma taɓarɓarewar al’amura a yankin Gabas Ta Tsakiya. Angela Merkel dai, ta yi kira ga hukumomin ƙasashen yankin Gabas Ta Tsakiyan, da su yi duk iyakacin ƙoƙarinsu, wajen kwantad da ƙurar rikicin da ya ɓarke.

Daga nan Jamus dai, shugaba Bush, zai tashi ne zuwa ƙasar Rasha, inda zai halarci taron ƙoli na shugabannin ƙasashen rukunin G-8 a birnin St.-Petersburg.