Shugaba Bush Ya fuskanci bore a Japan | Labarai | DW | 15.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bush Ya fuskanci bore a Japan

Mutane a kalla dari hudu ne birnin Kyoto na kasar Japan suka gudanar da zanga zangar nuna adawa da matakan da shugaba Bush ya dauka a kann kasar Iraqi da Afghanistan.

Wannan zanga zanga dai tazo ne a dai dai lokacin da shugaban na Amurka ya iasa kasar ta Japan don fara ziyarar aiki ta tsawon mako guda a wasu kasashe dake yankin Asia.

Masu zanga zangar dai sun bukaci shugaban na Amurka daya gaggauta janye dakarun sojin su daga wadan nan kasashe biyu bisa irin asarar rayukan da akeyi a kullum ranar Allah ta´ala.

A gobe ne dai ake sa ran shugaban na Amurka zai gana da Faramiya Koizumi,kafin wucewar sa izuwa ragowar kasashen da aka shirya cewa zai kai ziyarar a tsawon makon gudan.

Wadan nan dai kasashe sun hadar da kasar Sin da Koriya ta kudu da kuma kasar Mongolia.