Shugaba Bush ya fara ziyarar aiki a janhuriyar Czeck | Labarai | DW | 05.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bush ya fara ziyarar aiki a janhuriyar Czeck

Shugaban Amirka GWB ya isa Prague babban birnin janhuriyar Czeck a matakin farko na rangadin kwanaki 8 a nahiyar Turai. An shirya Bush zai gana da shugaban Czeck Vaclav Klaus da FM Mirek Topolanek, wadanda dukkansu biyu ke goyon bayan shirinsa na gina kandagarkin makami mai linzami a janhuriyar ta Czeck da kuma Poland. Shirin dai ya sha suka da kakkausan lafazi daga shugaban Rasha Vladimir Putin, wanda ake sa rai zasu gana a kebe da Bush a lokacin taron kolin kungiyar G8 da za´a fara gobe a Heiligendamm dake nan Jamus.