1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bush ya ce za´a samu hadin kai da ´yan Democrat

Shugaban Amirka GWB ya ce asarar iko da jam´iyarsa ta Republican ta yi a zabukan ´yan majalisun dokoki ba zata shafi manufarsa ta yaki da ta´addanci ba. A cikin jawabinsa na mako mako ta gidan radiyo wanda ya zo daidai da ranar tuanawa da tsofaffin sojin Amirka, shugaba Bush ya hakikance cewa Amirka zata samu galaba kan abokan gabanta. Tun bayan kashin da jam´iyarsa ta sha a zaben na rabin wa´adi Bush ya yi ta ganawa da manyan shugabannin democrat a wani mataki na samun cikakken hadin kai. A cikin jawabin sa Bush cewa yayi.

“An kammala zabukan, amma har yanzu ba mu rabu da matsalolin ba, saboda haka ina tabbatarwa ´yan majalsiar dattawa cewar zamu ba da cikakken hadin kai yadda ya kamata domin warware matsalolin da muka fuskanta gaba dayan mu.”