Shugaba Bush ya ce ba´a kawo karshen yaki da tarzoma ba | Labarai | DW | 12.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bush ya ce ba´a kawo karshen yaki da tarzoma ba

Shugaban Amirka GWB yayiwa al´umar A mirka jawabi daga fadar White House yana mai cewa ba´a kammala yakin da ake yi da ta´addanci ba. A cikin jawabin shugaba Bush ya kare yakin da Amirka ke jagoranta a Iraqi sannan ya yi kira da a kara hada kai don samun galaba akan ayyukan ta´addanci. Bush ya kwatanta yaki da ta´addancin da cewa wata gagwarmaya ce ta wayewar kai wanda ya zama tilas a ci-gaba da yi har sai an ga karshen sa. Ya ce idan ba´a yi haka tamkar an mika kai ga abin da ya kira ´yan mulkin kama karya na GTT masu mallakar makaman nukiliya. Jawabin na Bush ya zo ne a daidai lokacin da ake bukukuwa da addu´o´i na cika shekaru 5 da kai hare haren ta´addancin ranar 11 ga watan satumba a Amirka. Sa´o´i kadan gabanin bukukuwan mataimakin shugaban kungiyar al-Qaida, Ayman al-Zawahiri yayi gargadin cewa kasashe yankin tekun Fasha da Isra´ila su ne nan gaba kungiyar al´Qaida zata kaiwa hari. A cikin wani sakon bidiyo al-Zawahiri yayi kira ga musulmi da su tsananta nuna adawa da Amirka.