Shugaba Bush ya bukaci amincewar majalisa akan kudin aikin soji da tsaro | Labarai | DW | 21.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bush ya bukaci amincewar majalisa akan kudin aikin soji da tsaro

Bush/Terror

Shugabnan Amurka Geroge W Bush ya bukaci majalisar dattawan kasar .data amince da bukatar samar da kudi gaaikin sojijojin ksar wanda ya hada da yakin Iraqi,sannan kuma su sabanta shirinnan da ya jawo cece kuce na dokkin da suka shafi yaki da taaddanci.

Shugaban ya shedawa manema labarai a fadar white House cewa yan tadda suna shirin sake kawo musu farmaki , adon haka ya zama dole su tanadi abubuwan da zasu kare alummar Amurka.

Shugaban ya yi kiran ne a yayin da su kuma yan majalisar suke duba kasafin kudin kasar na tsaro na shekara shekara da kuma dubawa ko lalle akwai bukatar sabunda ddoklar kishin kasa dokar data kunshi matakan karfafa tsaro wadanda aka dauka bayan ankaiwa Amurka harin sha daya ga watan satumba, kafin waadinsu ya kare a karshen shekara.

A dai dai lokacin zaman majalisar dattawanne kuma mataimakin shugaba Bush Mr Dick Cheney ya katse ziyarar da yake y a gabas ta tsakiya,inda ya halarci zaman majalisar ya kada kuriar da ta raba gardama a bukatar da gwamnati ta mika rage gibin kasafin kudin.

Mr Cheney ya dai kada kuriarne a matsayin shugaban majalisar dattawan Amurkan.