Shugaba Bush ya amince sabuwar dokar da ta haramta azabtar da firsinoni | Labarai | DW | 16.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bush ya amince sabuwar dokar da ta haramta azabtar da firsinoni

Shugban Amirka GWB ya ba da kai a takaddamar da suke yi da ´yan majalisar dokoki game da haramta azabtarwa da cin zarafin wadanda ake tsare da su bisa laifin ayyukan ta´addanci. Bayan ta shafe watanni tana nuna adawa yanzu haka gwamnati ta amince da dokar da ta haramta ganawa da kuma kaskanta mutanen da ake tsare da su bisa zargin aikata ta´addanci a ciki da wajen Amirka. Dan malajisar dattijai na jam´iyar Republican John McCain ya gabatar da shirin dokar. Shugaba Bush ya ce wannan mataki da aka dauka ya nuna a fili cewar gwamnatin sa ba ta amince da cin zarafi ko azabtar da firsinoni a ciki da wajen Amirka ba. Da farko gwamnati ta yi barazanar hawa kujerar naki don hana yiwa dokar gyaran fuska. To amma mafi rinjaye daga cikin wakilan majalisun dokokin sun goyi da bayan shawarar da McCain ya gabatar, wanda kanshi aka taba cin zarafinsa lokacin da yayi zaman kurkuku na tsawon shekaru biyar a Vietnam.