1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bush na kan hanyar sa ta zuwa Indonesia

A wani lokaci ne a nan gaba kadan a yau, ake sa ran isar shugaba Bush na Amurka kasar Indonesia, don fara wata ziyarar aiki.

Rahotanni daga babban birnin kasar wato Jakarta, na tabbatar da cewa dubbannin mutane ne suke gudanar da zanga zangar yin Allah wadai da matakan Amurka, musanmamma a Iraqi da kuma Afghanistan.

Ya zuwa yanzu dai bayanai daga kasar, na nuni da cewa tuni jami´an tsaron kasar suka fara binciken zargin cewa, wasu na son tashin bom a inda shugaban na Amurka aka shirya zai sadu da takwaransa na Indonesian , wato Susilo Bambang.

Wannan ziyara dai, itace ta farko da shugaban na Amurka ke kaiwa ga kasar data fi kowace kasa a duniya yawan mabiya addinin Musulunci.