Shugaba Bush na Amirka ya yi wa Majalisar dokoki jawabi a kan halin da kasar ke ciki. | Labarai | DW | 01.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bush na Amirka ya yi wa Majalisar dokoki jawabi a kan halin da kasar ke ciki.

Shugaban Amirka, George W. Bush ya yi wa Majalisar Dokokin kasar jawabi a kan halin da Amirka ke ciki. A cikin jawabin nasa dai, shugaba Bush ya nanata cewa, dakarun kasar da ke girke a Iraqi na samun nasara a yakin da suke yi da `yan tawaye masu gwagwarmaya da su. Sabili da haka ne dai ya yi watsi da duk wani kira na gaggauta janyewar sojojin kasar daga Iraqin. Bai dai ba da wani kayyadaden lokaci na janye dakarun ba, saboda yin hakan, kamar yadda ya bayyanar, zai kai abokan burmin Amirkan ne ya baro.

Shugaba Bush ya kuma yi amfani da jawabin ne wajen kalubalantar `yan jam’iyyar Democrats da wasu bangarori masu sukar gwamnatinsa da yaudarar jama’an kasar game da batun zargin da aka yi wa tsohon shugaban Iraqi, Saddam Hussein, da mallakar makaman nukiliya. Kazalika kuma, Bush ya nanata cewa, bai kamata a bar Iran ta iya sarrafa makaman nukiliya ba. Ya dai kuma yi kira ga kungiyar Hamas da ta juya wa duk wasu tashe-tashen hankulla baya, ta kuma amince da wanzuwar Isra’ila tamkar kasa.