Shugaba Bush na Amirka ya lashi takobin hawar kujera na ki a kan batun bai wa wani kamfanin Larabawa kwangilar kula da tashoshin jiragen ruwan Amirkan. | Labarai | DW | 22.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bush na Amirka ya lashi takobin hawar kujera na ki a kan batun bai wa wani kamfanin Larabawa kwangilar kula da tashoshin jiragen ruwan Amirkan.

Shugaban Amirka, George W. Bush ya ce zai hau kujerar na ki don yin adawa da duk wani yunkurin da majalisar dattijan kasar ke yi na hana wani kamfanin Larabawa samun kwangilar kula da tashoshin jiragen ruwan kasar. `Yan majalisar, na jam’iyyun Republicans da Democrats na daddge wa shirin ne, saboda a nasu ganin, hakan na dauke da wata kasada da ta shafi harkokin tsaro na kasar.

Amma shi shugaba Bush, ya nanata cewa kamfanin daga kasar Dubai, ba shi da wata jibinta da harkokin tsaro; kuma sai da aka yi nazarin duk wata kasada kafin a amince da bai wa kamfanin kwangilar, ta kula da muhimman tashoshin jiragen ruwa guda 6 na Amirkan. Masu sukar shirin dai na ganin cewa, zai iya janyo wata kasada ta kai hare-haren `yan ta’adda kwatankwacin na ran 11 ga watan Satumban shekara ta 2001. Sun kuma ce mutane 2 daga cikin `yan harin kunan bakin waken, `yan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ne.