Shugaba Bush na Amirka ya dawo gida bayan wata ziyarar gaggawa da ya kai a Iraqi.
June 14, 2006Shugaban Amirka, George W. Bush, ya dawo gida a birnin Washington, inda yake halartar shawarwari da manyan jami’an majalisar ministocinsa a sansanin Camp David, bayan wata ziyarar sirri da ya kai a Iraqi. Yayin ziyarar a birnin Bagadaza, shugaba Bush ya gana da sabon Firamiyan Iraqin, Nuri al-Maliki. A tattaunawar da suka yi dai, shugaban Amirkan ya tabbatar wa al-Maliki cikakken goyon bayansa, da kuma amincewa da gwamnatin da ya kafa da manufofin da ta sanya a gaba. Ziyarar Bush dai ta zo ne, ƙasa da mako ɗaya, bayan kashe shugaban ƙungiyar al-Qaeda a Iraqin da dakarun Amirkan suka yi, a wani harin da suka kai wa maɓuyarsa da jiragen saman yaƙi.
Tuni dai, ƙungiyar ta al-Qaeda, ta ba da sanarwar naɗa Abu Hamza al-Mahajer, tamkar wanda zai maye gurbin al-Zarqawi. Sabon jagoran ƙungiyar, ya lashi takobin ɗaukar fansa kan dakarun Amirka da kuma ’yan ƙasar Iraqin masu mara musu baya.