Shugaba Bus ya isa Bahrain | Labarai | DW | 12.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bus ya isa Bahrain

Shugaba Bush na Amurka ya isa Bahrain a ci gaba da rangadinsa zuwa ƙasashen larabawa. A Bahrain Bush ya baiyana cewa ƙasashen biyu suna da nauyi guda da ya rataya a wuyansu na tabbatar da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya. Bush ya taso ne daga Kuwait inda tun farko ya tattauna da komandan rundunar sojin Amurka a Iraƙi David Petraeus. Komamandan ya sanarwa da Bush cewa an samu ƙarin hare hare kan dakarun Amurka da ake ganin da bama bamai ne ƙirar Iran . Bush ya kara da cewa:

Bush,bayan wani jawabi da yayiwa sojojin Amurkan ya kuma baiyana cewa yana nan kan bakansa na rage yawan sojojin Amurka a Iraƙi nan zuwa watan Yuli. Yace hakan yana nuni da cewa manufofin Amurka a Iraƙi suna aiki. Bush ya fara wannan ziyara ce daga kasar Isra’ila da yankin yamma da Gaɓar kogin Jordan. Ana kuma sa ran zai wuce zuwa haɗaɗɗiyar daular larabawa da Saudiya kafin ya yada zangonsa na ƙarshe a ƙasar Masar ranar Laraba.