1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin 2017

December 14, 2016

A yunkurinsa na fitar da kasar cikin masassara da tai mata tarnaki, da ranar Laraban nan Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi na sama da Naira tiriliyan bakwai.

https://p.dw.com/p/2UHLK
Präsident von Nigeria Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Sabon kasafin da ke zaman irinsa mafi girma kuma ke da burin fitar da kasar zuwa tudun mun tsira dai ya kunshi Naira tiriliyan biyu da miliyan dubu dari biyu da arba'in ko kuma kaso 30.7 domin manya na ayyukan raya kasa, sannan kuma da tiriliyan biyu da miliyan dubu dari tara da tamanin domin harkokin yau da na gobe.

Ma'aikatar ayyuka da gidaje da wutar lantarki ce ta tashi da kaso mafi tsoka na Naira miliyan dubu 529, a yayin kuma da 'yar uwarta ta sufuri ke zaman ta biyu da miliyan dubu 262.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

A badin dai za'a kashe Naira miliyan dubu140 domin harkoki na tsaro sannan da miliyan dubu 92 wajen harkokin noma. Ma'aikatar ruwa dai ta tashi da Naira miliyan dubu 85 da nufin manya na ayyukan a yayin da kuma shirin afuwar tsagerun yankin Niger Delta zai lamushe Naira miliyan dubu 65. Kokarin sake ginin yankin Arewa maso Gabas ya samu Naira milliyan dubu 45 daga gwamnatin.

 A badin dai kuma a fadar shugaban kasar da ya mika kasafin ga zama na hadin gwiwar majalisun kasar biyu dai, tarrayar Najeriya za ta mayar da hankali ne ga kokari na sake ginin bukatu na rayuwar al'ummar da ta fara a bana. Wani abun kuma da ya dauki hankali cikin kasafin na zaman wasu Naira miliyan dubu 565 da aka karbo a hannun barayi na kasar kuma ake shiri na kasheta a shekarar da ke tafen.