Shugaba Buhari ya dakatar sakataren gwamnatinsa
April 19, 2017Talla
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dakatar da sakataren gwamnatin kasar Babachir David Lawal da kuma shugaban hukumar tara bayanan sirri Ambassada Ayo Oke da ake zargi cikin wasu jerin badakalar cin hanci.
Shugaba Buhari ya kuma kafa wani kwamitin mutane uku karkashin mataimakin shugaban kasar domin bincike da mika rahoto cikin tsawon makonni biyu.