1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Najeriya ya rantsar da ministocin gwamnatinsa

Ubale Musa/ MNANovember 11, 2015

A wani matakin kama hanyar gina ginshikan cikon alkawarin sauyi, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da jerin ministocin da ke zaman manyan limaman sauyi na gwamnatinsa.

https://p.dw.com/p/1H4DV
Nigeria Kabinett Muhammadu Buhari Präsident
Hoto: Reuters/A.Sotunde

A wani bikin rantsuwar da ya samu halartar daukacin masu ruwa da tsaki da batun mulkin kasar ta Najeriya da a ranar Laraba a birnin Abuja Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bayyana sunaye da ma'aikatu na sabbabin ministocin kasar da aka jima ana jira.

Sabuwar majalisar ministocin mai wakilai 36 dai ta kunshi manyan ministoci 23 da kuma wasu kanana 13. Sannan kuma an rage yawan ma'aikatu na gwamnatin kasar daga 38 zuwa 24 da nufin rage kisan kudi da ma dora kasar bisa saiti.

Bikin dai na zaman matakin farko na kaiwa ga fara aiwatar da alkawarin sauyi na sabuwar gwamnatin a bangaren shugaban kasar da ya share watanni dai dai har guda biyar yana ta jan kafa.

Alkawari kaya inji masu iya magana

Sabuwar majalisar dai na da jan aikin cika alkawarin da ya kai ga kare mulkin 'yan lema na shekaru 16, da haihuwar fata na samar da zuma da madi ga kasar da ke kallon arziki a gaban gida amma kuma yunwa a ciki.

Paris Medef Zentrale Buhari Gattaz
Hoto: Getty Images/AFP/E. Piermont

Ministocin na Buhari dai sun dau ragama a lokacin da arzikin man fetir din da kasar ke dogaro da shi ta rayuwa ke kasa a cikin kasa ga farashi, sannan kuma fata na 'yan kasa ke sararin samaniyar sama. Abun da a cewar Buharin ya sanya gwamnatin sauya alkibla zuwa gabas da nufin neman mafita ga kasa.

"A cikin rushewar farashin man fetur mun yi hobbasar fadada tattalin arziki zuwa ga harkar domin samar da aikin yi da kuma shiga harkar ma'adinai na karkashin kasa domin samun kudin shiga. Babban burinmu shi ne isarwa kai ga kayan abinci irinsu shinkafa da alkama, sannan kuma mu zamo manyan masu amfana da kuma fitar da wadannan hajjoji da kuma ma'adinai."

Ko ma ta ina suke shirin fitar da matsatsen wandon dai, tuni ra'ayi na bambamta a tsakanin na ministocin bisa hanyar sauke nauyin da ke tsaka na kawunansu a yanzu.

Samar da aikin yi ga mata da matasa

Aisha Alhassan dai na zaman sabuwar ministar matan kasar ta Najeriya da kuma ke da burin samar da abun yi a tsakanin mata da matasa.

"Akwai abubuwa da yawa da za a kirkiro yadda za a taimaka wa 'ya'yanmu da matanmu su samu sana'o'in yi domin a rage talauci. Sannan maganar rage matsalar cin hanci da rashawa, daga kan babba ya kamata a fara ganin misali. Idan kai ka kiyaye to duk wanda ke kasa da kai za ka iya kwabanshi."

Nigeria Babatunde Fashola
Babatunde Fashola shi ne ministan makamashi, ayyuka da kuma samar da gidajeHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi

Ga Abdurahman Dambazau da tun da farko aka dauka zai zamo minista na tsaro amma kuma ya kare da cikin gida dai wai nadin bai zo a cikin mamaki ba.

"Babum mamaki saboda shi shugaban kasa duk ya sanmu. Ya san abinda kowa zaim iya yi. Kuma shugabanci ne na tafiyar da sha'anin gwamnati. Don an nada ka minista ba kai kadai za ka yi aikin ba."

To sai dai a tunanin Abubakar Malami da ke zaman sabon ministan shari'a, al'ummar kasar suna shirin ganin sauyi babba a cikin harkar shari'a ta kasar.

"Idan bangaren shari'a ya zama ba shi da kyakkyawar alkibla da fahimtar ainihin tsayuwa a kan gaskiya da kuma yin aiki da ita da kuma gani an yi da'a a dukkan fannonin dokokin kasa, to ba inda za a."

Abun jira a gani dai na zaman kamu na ludayi na ministocin da tuni suka kammala zamansu na farko suka kuma ce sun shirya tsaf domin sauyin da 'yan kasa ke doki na gani yanzu.