1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Assad yayi barazanar rufe kan iyaka da Lebanon

Zainab A MohammedAugust 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5q

Syria tayi barazanar rufe kan iyakokinta da Lebanon,idan har an tura dakarun kiyaye zaman lafiyan mdd a yankin,batu dake dada kawo rudani a kokarin da kasashen duniya masu fada aji keyi na cimma yarjejeniyar tura ayarin jamian tsaro da zasu taimaka wajen cimma zaman lafiya,sakamakon tsagaita wuta tsakanin Izraela day an Hizbolla na Lebanon.

Wannan gargadi na Syria dai yazo ne adaidai lokacin da jakadun Eu ,suka shiga rana ta biyu a tattaunawar sharan fagen ,taron ministocin harkokin wajen kungiyar da zaa gudanar gobe a birnin Brussels din kasar Belgium,taron da zai samu halartan sakatare general na Mdd Kofi Annan.Kawo yanzu an fara samun kwarya kwaryar daidaito adangane da tura sojoji daka kasashen Turan.Rahotanni daga birnin Parin na nuni dacewa Faransa zata dada tura sojoji guda 100,domin hadewa da kimanin 400 data rigaya ta tura Lebanon .Shugaba Bashar Al-Assad na Syria yayi gargadin cewa tura ayarin dakarun kiyaye zaman lafiya,kamar yadda mdd ta cimma a kudurin tsagaita wuta a ranar 14 ga wannan wata na Augusta,zai zame wa kasarsa barazana.