1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Assad ya ce ba zai gabatar da kansa ga masu bincike ba

A lokacin da yake ambaton ´yancin Syria, shugaba Bashar al-Assad ya ce ba zai gabatar da kansa don amsa tambayoyi daga jami´an MDD dake bincike kisan gillar da aka yiwa tsohon FM Libanon Rafik Hariri ba. A wani jawabi da yayiwa kungiyar lauyoyin Larabawa Assad ya ce duk da haka zai ci-gaba da ba da hadin kai ga binciken da kasashen duniya ke yi. Assad ya ce batun kare ´yancin Syria shi ne mafifici akan duk wani bincike na MDD. Jami´an MDD sun ce Syria ba ta ba da hadin kai yadda ya kamata. Tsohon shugaban masu binciken kuma mai shigar da kara na Jamus Detlev Mehlis ya zargi manyan jami´an leken asirin Syria da na Libanon da hannu a kisan da aka yiwa Mista Hariri a cikin watan fabrairun bara.