Shugaba Arroy ta ba da umarnin gudanar bincike a wata turereniya | Labarai | DW | 04.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Arroy ta ba da umarnin gudanar bincike a wata turereniya

Shugabar Filipins Gloria Macapagal Arroyo ta ba da umarnin gudanar da bincike a wata turereniya da ta auku wadda ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 73 sannan wasu 500 suka samu raunuka. An dai yi turereniyar ne lokacin da mutane suka yi dafifi a wajen filin wani wasa dake birnin Manila, don halarta wani wasan telebijin mai farin jini ga ´yan kasar. Shugabar ta umarci hukumomin da su ba da cikakken rahoton binciken cikin sa´o´i 72. Rahotanni sun ce mutane kimanin dubu 30 suka hallarar a filin wasan don ganewa idonsu yadda zata kaya a wasan na telebijin. Daukacin wadanda hadarin ya rutsa da su tsofaffi ne, wadanda suka shafe kwanaki da dama suna kwana a wajen filin wasan.