1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Abbas ya baiyana matakin sojin Isra´ila a Gaza da cewa kisan kare dangi ne

January 16, 2008
https://p.dw.com/p/CqG0

Bayan mummunan harin da sojin Isra´ila suka kai a Zirin Gaza shugaban Palasɗinawa Mahmud Abbas ya nuna shakku dangane da aniyar Isra´ila ta samun zaman lafiya. Shugaba Abbas ya faɗawa manema labarai a birnin Ramallah cewa irin wannan kisan ƙare dangi ba zai taɓa samar da zaman lafiya ba. Ita ma ƙungiyar tarayyar Turai EU ta nuna damuwa dangane da halin da ake ciki sannan ta yi kira ga sassan biyu da su daina tashe tashen hankula kana kuma su ci-gaba da tattaunawar da suka fara. Wata rundunar sojin Isra´ila ta musamman ta ce ta yi musayar wuta da wasu sojojin sa kai na Palasɗinu wadanda suka harba rokoki cikin Isra´ila, inda ta kashe Palasɗinawa 19 sannan ta jiyawa fiye da mutane 50 rauni. Daga cikin waɗanda aka kashe akwai fararen hula da kuma dan shugaban kungiyar Hamas kuma tsohon ministan harkokin waje Mahmud al-Sahar.