Shugab adawa a Tanzania yace bai yarda da sakamakon zabe ba | Labarai | DW | 19.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugab adawa a Tanzania yace bai yarda da sakamakon zabe ba

Shugaban adawa na kasar Tanzania, wato Ibrahim Lipumba yace akwai magudi a cikin sakamakon zaben daya bawa Mr Jakay Kikwete nasara a zaben shugaban kasa da aka gudanar a makon daya gabata.

Duk da wannan zargi da shugaban adawar yayi babu wata gamsasshiyar hujja daya bayar dake nuni da cewa an tafka magudi a cikin sakamakon zaben.

Ibrahim Lipumba daya zo na biyu a yawan kuriun sakamakon zaben shugaban kasar, yaci gaba da cewa suna cikin rudani dangane da hanyoyin da aka bi aka gudanar da wannan magudi.

Wadan nan kalaman dai na Ibrahim Lipumba sun biyo bayan sanarwar da hukumar zaben kasar ta bayar ne na cewa Mr Jakay Kikwete ne ya lashe zaben shugaban kasar da kusan kashi tamanin cikin dari.

Ya zuwa yanzu ma dai tuni shugaban adawar ya mika koken sa a gaban kotu na hana abokin karawar sa, bayyana kansa a matsayin wanda yayi nasara.

Da yawa dai daga cikin masa sa ido daga ketare sun yabi yadda wannan zabe ya gudana da cewa an gudanar dashi cikin lumana da kwanciyar hankali, ko da yake an fuskanci wasu yan rigingimu a yankin Zanzibar.