Shubaga Bush ya isa Argentina don halartar taron kolin kasashen nahiyar Amirka | Labarai | DW | 04.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shubaga Bush ya isa Argentina don halartar taron kolin kasashen nahiyar Amirka

A cikin tsauraran matakan tsaro shugaban Amirka GWB ya isa kasar Argentina inda zai halarci taron kolin kasashen nahiyar Amirka. Shugabannin kasashe 34 daga arewaci da kudancin Amirka ke halartar taron kolin, inda zasu tattauna akan matakan kirkiro sabbin guraben aikin da nufin yaki da matsalolin talauci sannan a lokaci daya kuma a karfafa mulkin demukiradiya a nahiyar baki daya. To sai dai wani batun da za´a mayar da hankali a kai shi ne wani shirin da Amirka ke yi na kafa wani yankin ciniki maras shinge a fadin nahiyar Amirka baki daya. Ana dai ta da jijiyar wuya dangane da wannan shiri. Kasar Mexiko na matsa lamba don samun wani ci-gaba yayin da shugaba Hugo Chevez na Venezuella yayi kira da a yi watsi da wannan shiri gaba daya a taron koli wanda zai gudana a birnin Mar del Plata.