Shuagabannin Palasdinawa sunyi kira da dakatar da fada tsakanin magoya bayansu. | Labarai | DW | 19.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shuagabannin Palasdinawa sunyi kira da dakatar da fada tsakanin magoya bayansu.

Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas da Firamiminta Ismail Haniyeh sunyi kira ga magoya bayansu dake yaki da juna da su dakatar da fada tsakaninsu saboda zaman lafiya da hadin kann yankin.

Cikin wani jawabi da yaiwa gidan TV Haniye wanda ke jagorancin gwamnatin Palasdinawa karkashin Hamas yace kra da a gaggauta gudanar da zabe da shugaba Mahmud Abbas yai a matsayin hanya ta kawo karshen rikici tsakanin bangaraorin biyu,baya bisa tsarin mulkinsu.

Haniyeh yai wannan kira ne bayan akalla mutane 5 sun rasa rayukansu cikin bata kashi tsakanin magoya bayan kungiyar Hamas da Fatah a birnin gaza a yau talata.

Akalla kuma mutane 18 suka samu raunuka,cikinsu har da yara kanana yan makaranta.