Shuagaba Ortega ya lashe zaɓen Nicaragua. | Siyasa | DW | 08.11.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shuagaba Ortega ya lashe zaɓen Nicaragua.

A halin yanzu dai an sami ƙarin haske kan sakamakon zaɓen da aka gudanar a ƙasar Nicaragua; bayan ƙirga fiye da kashi 91 cikin ɗari na ƙuri’un da aka ka da, an tabbatar cewa, tsohon shugaban juyin juya hali na ƙasar, Daniel Ortega ne ya lashe zaɓen.

Daniel Ortega, shugaba mai jiran gado na Nicaragua.

Daniel Ortega, shugaba mai jiran gado na Nicaragua.

Daniel Ortega, wanda ya jagoranci gwamnatin ’yan Sandinista, da suka yi juyin juya halin nan a ƙasar Nicaragua, tun fiye da shekaru 25 da suka wuce, ya sake hawa karagar mulkin ƙasar a zaɓen da aka gudanar a wannan makon. Sau uku dai, Ortega, ya tsaya takarar zaɓen shugaban ƙasar, amma ya sha kaye. A wannan karon kuwa, sai ga shi ya sami nasara.

Shi dai Daniel Ortega, tun a cikin shekarun 1970 ne ya fara nuna adawa ga shugaban mulkin kama karya, Anastasio Somoza. Daga baya ma, shi ne ya jagoranci ’yan yaƙin sunƙurun Sandinista, waɗanda suka hamɓarad da gwamnatin shugaba Somozan. A nan ne kuma ya zamo shugaban ƙasa. Amma gwamnatinsa ba ta sami damar ci gaba da ayyukan raya ƙasar ba, saboda ta sha gwagwarmaya ne da ’yan sari ka noƙen Contras, waɗanda Amirka ke ɗaure wa gindi. A 1990 ne dai ’yan Sandinistan suka sha kaye a zaɓen da aka gudanar. Tun daga nan ne kuma ’yan jari hujja suka shiga jan ragamar mulkin ƙasar. Amma hakan bai janyo wata fa’ida ga talakawan ƙasar ba. Kai za a iya cewa sai ƙara talaucewa ma ’yan ƙasar suka yi. Goshin zaɓen baya-bayan ne dai, an ce duk mutane uku bisa huɗu a ƙasar na huskantar bala’in talauci.

A unguwan marasa galihun ne kuwa, shugaba mai jirag gado Daniel Ortega ke da mafi yawan magoya bayansa. Ko me ya sa haka? Wasu mazauna unguwar, sun bayyana dalilin nuna goyon bayansu ga Ortegan ne da cewa:-

„Saboda a ko yaushe tare da mu talakawa yake. Shi ko abokin hamayyarsa, Montealegre, tare da ’yan jari hujja yake hulɗa. Masu bin aƙidar jari hujjan dai ’yan damfara ne, kamar Mafiya, amma waɗanda Amirka ke goyon bayansu. Mu dai mun ɗora wa Amirka ne , duk laifin wannan wahala da muke huskanta, saboda ita ce ke ɗaure wa masu kama karya kamarsu Somoza da Eduardo Montelegre gindi.“

A lokacin yaƙin neman zaɓe dai, Ortega taka tsantsan ya yi. bai yi ta fira da maneman labarai ko ta yaya ba, kuma da wuya ka ga ya shiga cikin wata muhawara. A cikin farkon jawabinsa bayan da aka fara bayyana sakamakon zaɓen dai, Ortega ya bayyana cewa:-

„Ina godiya ga Allah, wanda ya ba mu wannan damar ta gudanad da kyakyawan yaƙin neman zaɓe da kuma bayyana burin da muka sanya a gaba; wato tabbatad da zaman lafiya, da samar wa jama’a aikin yi, da kuma haɗa kan al’umman ƙasar nan. Babu shakka, nan ba da daɗewa ba, za mu shiga cikin wani yanayi na adalci, da kuma nuna zumunci a fannin tattalin arzikinmu. Ta hakan ne Nicaragua za ta sami bunƙasa. Ƙasarmu kuma za ta sammi farfaɗowa, ta yadda za a iya kwatanta ta da kyakyawar juyin juya hali na addini.“

Wasu masharhanta dai na ganin cewa, Daniel Ortga, zai fi karkata ne zuwa ga shugaban ƙasar Venezuela, Hugo Chavez. Tuni dai Venezuelan ta tura manyan jiragen ruwa guda biyu, ɗauke da ɗaruruwan tan na man fetur zuwa tashar jirgin ruwan Nicaraguan. Ta ce kuma, wasu na kan hanya suna zuwa. Tare da Daniel Ortega dai, masharhantan na ganin cewa, an sami wani abokin burmin shugaba Chavez na Venezuela ke nan, a jerin ƙasashen da ke adawa da manufofin gwamnatin fadar White House a Latin Amirka. Masu ka da ƙuri’u a ƙasar Nicaraguan kam sun sha bayyana fatar isowar wannan lokacin:-

„Ortega zai iya kyautata halin rayuwa a Nicaragua, ta dogaro kann hulɗoɗin da yake da su a ƙasashe da dama na ƙetare, waɗanda kuma ke goyon bayansa, alal misali, Chavez ko kuma Kuba.“

Ko wane irin zargi za a yi musu dai, ’yan ƙasar Nicaraguan na ganin cewa, sanya alamar da shugaba Hugo Chavez na Venezuela ya yi na turo musu jiragen ruwa ɗauke da man fetur, wato wani mataki ne na tallafa wa ƙasarsu, da kuma rage musu wahalhalun da suke ta fama da su.

 • Kwanan wata 08.11.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtxU
 • Kwanan wata 08.11.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtxU