Shirye-shiyen Britania na kai hari ga Iran | Labarai | DW | 02.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirye-shiyen Britania na kai hari ga Iran

Jaridar Sunday Telegrahp, ta ƙasar Britania, ta fito wani labari a yau lahadi, a game da shirye shiryen gwamnatinTony Blair, na kai farmaki a ƙasar Iran.

Jaridar ta ce gobe ne, idan Allah ya kai mu, gwamnati za tayi wani zaman taro na sirri, domin tunani, a kan mattakan kai harin, don cilasta wa Iran, yin watsi da aniyar ta, ta ƙera makamman nuklea.

Jaridar tace, majajiyar da ta tsegunta mata wannan labari, ta tabbatar cewa, babu makawa, Amurika, tare da haɗin gwiwar Britania, da sauran ƙasashe, kamar su Isra´ila,za ta yaƙi Iran, muddun hukumomin ƙasar, su ka ka ƙi bin umurnin komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia.

A ranar alhamis da ta gabata ne, komitin ya ba hukumomin Iran, wa´adin kwanaki 30, na ta yi watsi da batun ƙera makaman nuklea.

Jaridar tace, wannan hari, zai kasance ta fannin amen bama- bamai, ta sararin samaniya, ga dukan tashoshin da Iran, ke samar da makamashin nuklea.

A halin da a ke cikin yanzu, ba bu batun kaiwa Iran farmaki irin na ƙasar Iraki, domin ba a kada gizo ba, ba a tado ƙoƙi, inji Jaridar Sunday Telegraph.