1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye shiryen zaben Zimbabwe

GwanduMarch 12, 2008

Masu sa ido sun fara isa Zimbabwe

https://p.dw.com/p/DNc8
Shugaban Zimbabwean Robert MugabeHoto: AP

Wata tawaga ta Ƙungiyar tattalin arziki na ƙasashen kudancin Afrika ( SADC) ta isa ƙasar Zimbabwe domin duba irin shirye shiryen da ke ƙasa gabannin zaɓɓuka na waƙilan majalisar dokoki tare da na shugaban ƙasa da zai gudana ranar 29 ga watan maris.

Jaridar Herald ta gwamnatin Zimbabwe ta ce yanzu haka jami'ai 50 daga ƙungiyar Tattalin arziki na kudancin Afirka SADC sun sauka birnin Harare, kuma ana sa ran wasu zasu biyo baya cikin 'yan kwannakin nan. A wata hira da jaridar ta yi da Babban darakta na SADC Tanki Mothae jim kaɗan da saukarsu, Mothae ya ce sun zo domin amsa gayyatar shugaba Robert Mugabe, kuma ko ma ba don wannan dalilin ba, wajibi ne ƙungiyar SADC ta turo wakilan ta sabili da kasancewar Zimbabwe memba cikin ƙungiyar.

Wannan karon Shugaba Robert Mugabe ya aika da goro gayyata zuwa ga ƙungiyoyi 47 wadanda zasu duba yadda zaɓen na ƙarshen wata zai kasance a ƙasar wadda duniya ta mayar saniyar ware sabili da zargi da ake yiwa gwamnati da yawan keta haƙin bil adama. Bayan SADC da ƙungiyar Tarrayar Afrika (AU) akwai Kungiyoyi daga ƙasashen Sin da Rasha da kuma ƙasar Iran, kasashe da ke ƙawance da gwamnatin shugaba Mugabe da zasu duba zaɓen. Makon da ya gaba ne ministan Harkoƙin Wajen Zimbabwe Simbarashe Mumbengegwi ya sanar cewar Zimbabwe bata gayyatar ƙungiyar Tarayyar Turai tare da Amirka waɗanda suka zargi gwamnatin shugaba Mugabe da tafka maguɗi a zaɓen da ya gudana a shekara ta 2002. Shi kansa shugaba Mugabe ya bayyana a fili cewar ƙasarsa bazata bawa ƙasashen yanmaci wata dama na shiga sharo ba shanu a harkokin siyasar ta ba.

Babban taron majalisa kan gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar, wanda ke da alaƙa da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama, ya soki matakin da gwamnati ta ɗauka na hana wasu ƙasashe da ƙungiyoyi hallartar zaɓen. Ƙungiyar ta bayyana hushinta a fili tare da cewar bai kamata a mayar da al'amuran zaɓe tamkar gayyata zuwa bukin murnar zagayowar ranar haifuwa ba, inda ake gayyatar 'yan uwa da abokan arziki kawai, kuma wannan abu ne wanda kamata ya yi Zimbabwe ta bar ƙofofinta buɗe ga duniya domin ƙauracewa zargi kamar yadda aka saba gani bayan zaɓɓukan shekarun baya. Makon da ya gabata ne shugaba Robert Mugabe ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe tare kafa dokar mayar da hannun jarin kampanoni na ƙasashen ƙetare ga hannun 'yan ƙasa kana ya keɓe kayyayakin noma da suka haɗa da taraktoci da dabbobi da yawansu ya kai dubu ɗari uku da aka baiwa manoma baƙar fata don tallafawa musu wajen noma abinci. Makon da ya gabata ne a karon farko Shugaba Mugabe ya fito fili ya amince da cewar ana fuskantar matsanancin hali na yunwa a ƙasar.

A jiya talata ne kuma ma'aikatar harkoƙin wajen Amirka ta gabatar da wani rahoto inda ta bayyana sunayen wasu ƙasashen Afirka da ke kan gaba wajen take haƙƙin bil adama. Rahoton ya ce shekara ta 2007 ita ce mafi muni a rayukan al'uman ƙasar Zimbabwe, inda inji rahoton gwamnatin shugaba Mugabe ta kame jami'an adawa dubu ɗaya da dari shida tare da tsaresu ba tare da sun aikata laifi ba.