1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye shiryen zabe a NIgeria

April 9, 2007
https://p.dw.com/p/BuO3

jam´iyyun adawa a Nigeria na ci gaba da tattaunawar kulla kawance domin tunkarar zabe na gama, da ake shirin yi nan da kwanaki biyar masu zuwa.

Irin wannan tattaunawa a cewar rahotanni na ci gaba da wakana ne a mataki na jihohi da kuma tarayya.

Daga cikin jihohin dake gudanar da tattaunawar kawancen sun hadar da Delta da Oyo da kwara da Kogi da Adamawa da kuma Imo.

Ragowar sun hadar da Lagos da Ogun da Kebbi da Benue da Taraba da kuma Sakkwato.

Kafafen yada labarai dai sun rawaito mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar na jam´iyyar Ac na cewa, jam´iyyar sa zata hada karfi da jam´iyyun adawa,don kawar da mulkin jam´iyyar PDP mai mulkin kasar daya kira na kama karya.

Idan dai an iya tunawa, jam´iyyar ANPP ta kulla kawance da jam´iyyar Ac don ganin cewa sun lashe zabubbukan da ake shirin yi nan da yan kwanaki kalilan masu zuwa.

Za dai a gudanar da zaben gwamnoni na jihohi da kuma yan majalisun jihohi ne a ranar 14 ga watannan. Shi kuwa zaben shugaban kasa dana yan majalisun tarayya zai gudana ne a ranar 21 ga watan nan.